Game Da Cibiyar Ar-Rayhan

Game Da Cibiyar Ar – Rayhan

Wannan cibiya, wadda ke karkashin jagorancin Dr. Abubakar Muhammad Isa, cibiya ce da ta himmatu wajen samar da litattafan Addinin Musulunchi, ko dai ta hanyar yin bincike (research) don samarwa, ko kuma ta hanyar fassara wani littafi mai matukar muhimmanci ga al’ummar musulmi.

Cikin litattafan da binciken wannan cibiya ya samar akwai: Fayyataccen Bayani akan Siffar Sallar Annabi (S.A.W) da Kurakuren Masallata.

Cikin litattafan da wannan cibiya ta fassara aka kuma dabba’a akwai: Wasu Daga Cikin Halayen Magabata, Fassarar Littafin Ahlari Da Sharhi, da Nau’i’kan Zikiran Salla.

Founder - Dr. Abubakar Muhammad Isa

Dr. Abubakar Muhammad Isa

Danna Nan Don Karanta Tarihin Mawallafin

Mawallafin wannan shafi mai albarka sunansa Dr. Abubakar Muhammad Isa, dan asalin jahar Kano Najeriya. An haife shi a shekarar Miladiyya a ranar 30/4/1983. Bayan karatun allo da haddar Qur’ani mai girma a shekarar 1997, ya yi makarantar Firamare da Sakandare a Kano. Har ila yau, ya halarci Kwalejin share fagen shiga Jami’a (CAS Kano) a shekarar 2006. Haka kuma ya sami shaidar karamar Diploma a kan horon Malanta da Harshen Larabci da harkokin addinin Musulunci a shekarar 2007. Ya kammala digirinsa na farko a Jami’ar Bayero da ke Kano shekarar 2011, haka kuma ya samu shaidar kwarewa ta Malanta a Kwalejin Tarayya da ke Kano (FCE Kano) a shekarar 2015 (Yusuf Maitama University Of Education Kano). A shekar 2012 ya zama malami a Kwalejin Musulunci da Shari’a ta Kano a sashen nazarin harkokin Musulunci (Islamic Studies Department). Ya kammala digirinsa na biyu a Jami’ar Jazera da ke qasar Sudan a shekarar 2020. Ya kammala Digirin digri-gir (Ph.D), a Jami’ar Assalam da ke Kharthoum babban birnin qasar Sudan a shekara ta 2024. Ya zama mataimakin shugaban sashen Musulunci (Deputy H.O.D Islamic Studies Department), a kwalejin shari’a da Musulunci ta Jihar Kano (Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies) a shekarar 2024. A yanzu kuma shi ne shugaban sashen addinin Musulunci a kwalejin, (H.O.D) Islamic Studies Department. Wasu daga shedar kwarewa ta musamman sun hada da Ijaza ta Tajwidi da cibiyar Al-azhar da ke Kano a shekarar 2003, da shedar haddar Qur’ani a Jami’ar Qur’ani da ke Sudan a shekarar 2020.